A ranar 7 ga watan Maris, 2015 wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a kan keken sa a kusa da kasuwar kifi dake Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya kashe aƙalla mutane 10.[1][2][3] Bayan haka kuma a hukumance an bayar da rahoton cewa, an kai wasu jerin hare-haren ƙwara biyar da ƴan ƙunar baƙin wake suka kai a rana guda a yankuna biyar na birnin. A cewar majiyoyi da yawa, an kashe mutane 58 sannan, sama da mutane 143 suka jikkata.[4][2][5]